Success Principles
KADA KA TSAYA KUSA DA NASARA
By Napoleon Hill
Wannan sashi yana koyar da muhimmancin dagewa a lokacin da mutum ya fuskanci cikas. A aikin sa ko A kasuwancin sa. An kawo labarin R. U. Darby da danginsa da suka kusa samun zinariya, amma suka daina hakowa a lokacin da suka gaji da rashin sakamako. Daga baya, wani ya nemi shawarar ƙwararre, sai aka gano cewa zinariyar tana kusa sosai da inda suka tsaya. Darasin ya nuna cewa mutane da yawa suna barin buri ko business ɗinsu ne a lokacin da suke kusa da samun nasara. Wani lokaci matsala ba tana nufin ƙarshe ba ne; tana iya zama alama cewa mutum yana bukatar ƙarin ilimi, shawara, haƙuri, ko sabon tsari.
Main Message
Babban saƙon wannan sashin shi ne: kada mutum ya yi saurin dainawa saboda ya fuskanci ƙalubale na ɗan lokaci. Sau da yawa nasara tana zuwa ne bayan mutum ya yi haƙuri, ya nemi shawara, ya gyara tsari, kuma ya ci gaba da ƙoƙari lokacin da wasu suka riga suka fid da rai.